Majalisar tsaron Sudan ba ta amince da batun tsagaita wuta ba tare da janyewar RSF ba

Majalisar Tsaro ta Sudan ta ƙi amincewa da duk wani shirin tsagaita wuta, tana mai gindaya sharadin cewa sai dai idan (RSF) ta janye daga

Majalisar Tsaro ta Sudan ta ƙi amincewa da duk wani shirin tsagaita wuta, tana mai gindaya sharadin cewa sai dai idan (RSF) ta janye daga biranen da ta kwace iko da su.

Majalisar ta bayyana wannan matsayin ne a wani taro da aka gudanar a babban birnin Khartoum, don mayar da martani ga shawarar tsagaita wuta da Amurka ta gabatar.

A cewar majiyoyin, majalisar ta yanke shawarar ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kuma yin gangami don tunkarar abin da ta bayyana a matsayin “tawaye da makirci.” Majalisar ta kuma yi kira da a kafa sojojin sa kai na al’ummar kasa don tallafawa sojoji wajen tunkarar  RSF.

Wata majiya ta shaida wa Al-Mayadeen cewa Sojojin Sudan suna yin gagarumin shirin yaki a bangarorin Kordofan da Darfur. Rahotanni sun ce sojoji sun yi watsi  da tsagaita wuta har sai an sake kwace muhimman wurare daga hannun RSF.

Wani bayanin da ba a tabbatar da shi a hukumance ya yi nuni da cewa, Majalisar Tsaro ta Sudan, wacce shugaban Majalisar Mulkin Soja kuma shugaban rundunar sojojin Abdel Fattah al-Burhan ke jagoranta, za ta tattauna batun shirin tsagaita wuta da Amurka ta gabatar da nufin kawo karshen rikicin Sudan, a cewar wata majiya da ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran AFP.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments