Majalisar gudanar ta kutun ICC mai mambobi 125 ta sauya dokokin majalisar don samun damar tube Karim Khan babban mai gabatar da karan kotun wanda ya fidda samnacin kama jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Israil (HKI) wadanda suka hada da firai minista Benyamin Natanyahu da wasu ministocinsa.
ASP tana son cire Karim Khan ne a kan matsayinsa a ranar 24 ga wannan watan Yulin da muke ciki, tare da tuhume tuhume wadanda suka hada da fasadin jinsi mai kama da piyede ga wata ma’aikaciyar ofishinsa.
Jaridar Middle East Eye ta bayyana cewa Karin Khan ya musanta dukkan laifukan da ake tuhumarsa.
An zabi Karim Khan dan asalin kasar Pakistan amma wanda ya tashi a kasar Burtania, an kuma zabe shi a matsayin babban mai gabatar da kara na kotun ICC ne a watan Fabrairun shekara ta 2021 kuma shi ne na uku wanda ya rike wannan mukamin tun bayan kafa kotun a shekara ta 2002.