Majalisar dokokin kasar Yemen ta yi Allah wadai da yadda kasashen larabawa da na musulmi suka yi gum da bakunansu kana bun kunya da laifukan da Isra’ila ke yi kan al’ummar Falastinu a zirin Gaza, tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa domin dakile kisan kiyashin da gwamnatin kasar ke yi a yankin da aka yi wa kawanya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta yi kira ga majalisun kasashen Larabawa da na Musulunci da su gaggauta daukar matakin ceto al’ummar Falasdinu daga cin zarafi da Isra’ila ke ci gaba da yi, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 45,000 tare da jikkata wasu 107,000 a Gaza.
Majalisar ta ci gaba da sukar kalaman ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Sa’ar na neman ayyana magoya bayan Falasdinawa a matsayin ‘yan ta’adda, yana mai jaddada cewa ta’addanci na hakika yana bayyana a cikin laifuffukan da gwamnatin mamayar ke yi da kisan yara, mata da kuma tsofaffi.
Har ila yau, ta tabbatar da hakkin kasar Yemen na kare kai, zaman lafiyarta da diyaucinta ta dukkan hanyoyin da suka dace, tare da jaddada cewa kasar Larabawa za ta ci gaba da tinkarar duk wani harin da kasashen waje ke kaiwa kan kasar da yankunan ruwanta.
Har ila yau, ta yi Allah wadai da hare-haren da Amurka da Birtaniya da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Yemen, inda ta bayyana cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa da kudurorin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kuma suna yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.