Majalisar Dokokin Iraki Ta Bukaci Sanya Ranar Tunawa Da Qasim Sulaimani Da Abu-Mahdi Al-Muhandis

Majalisar Wakilan Iraki ta jaddada cewa: Ba za a manta da sadaukarwar da shugabannin kawo nasara suka yi ba wajen ‘yantar da al’ummar Iraki Mataimakin

Majalisar Wakilan Iraki ta jaddada cewa: Ba za a manta da sadaukarwar da shugabannin kawo nasara suka yi ba wajen ‘yantar da al’ummar Iraki

Mataimakin shugaban majalisar dokokin Iraki na farko Mohsen Al-Mandalawi a yau Juma’a ya bayyana cewa: Yau tsawon shekaru biyar ke nan da kisan gillar da aka yi wa shugabannin da suka kawo nasara ga al’umma tare da ‘yantar da su daga kangin ‘yan ta’adda da uwayen gijinsu Amurka a kusa da filin jirgin saman birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.

A sanarwar da ofishin Al-Mandalawi ya fitar ta bayyana cewa: Sadaukarwar da jagororin kawo nasara suka yi da kuma shekarun gwagwarmayar da suka yi har suka samu nasarar murkushe ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi da halatta jininsu da keta musu mutunci, baya ga irin gagarumin kokarin da suka yi wajen kare al’ummar Iraki da kuma wurare masu daraja al’amura ne da ba za a iya mantawa da su ba a tarihi.

Al-Mandalawi ya yi kira da a yi amfani da ranar zagayowar shahadar gwarazan al’ummar a matsayin ranar tunawa da gagarumin jarumtar shahidan biyu, Qasim Sulaimani da Abu Mahdi Al-Muhandis  da kuma sanar da al’ummar musulmi musamman matasa masu tasowa irin gudunmawar da manyan shugabannin biyu suka bayar wajen tunkarar girman kai da ta’addanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments