Babban jami’in raba agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher ya ce: “Hukumomin jin kai suna tattara kayayyakin agaji don fadada fara isar da su a fadin Zirin Gaza, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a yankin.”
Babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kare fararen hula da kayayyakin more rayuwa, da baiwa ma’aikatan agaji damar shiga cikin yankunan Gaza cikin koshin lafiya ba tare da janyo wata cikas ba wajen isar da kayayyakin ga masu bukata a duk wurin da suke a yankin.
Jami’in ya yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya yi amfani da muryarsa da nauyin da ya rataya a wuyarsa wajen dagewa cewa tsagaita bude wutar ta kasance mai dorewa, da mutunta hakkin dan Adam da kuma kawar da cikas ga ceton rayuka.