Majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta amince da doka wacce ta bukaci hukumar zabe ta yi amfani da na’urorin lantarki wajen tattara da kuma bayyana sakamakon zabuka da za’a gudanar a kasar, amma a duk lokacinda jami’an zabe a rumfunan zaben kasar suka kasa amfani da na’urorin to suna iya amfani da takarda mai lamba EC8A don isar da sakamako zabe da ita.
Kafin haka dai majalisar taki amincewa da hakan, saboda tunanin mafi yawan mutanen kasar basa son tsarin. Amma a yau Talata shugaban majalisar Godswill Akpabio ya gabatarwa majalisar bukatar a yiwa dokar zaben ta 60(3) gyra, bayan da sanata Mohammad Monguno (APAC, Borno ta Arewa) bulalar majalisar ya gabatar da bukatar a sake duba dokar. Mafi yawan yan majalisar dun amince da sauyin bayan an yiwa dokar gyara.