Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran waro Dr Ali Larijani ya isa birnin Mosco tare da sakon Jagoran juyinj juya halin musuluncin zuwa ga shugaba Putin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa sakon na jagora ga shugaban putin dangane da halin da ake ciki a yankin ne. Sannan sakon ya nuna yadda kasashen biyu suke aiki tare don fuskantar barazanar kasashen yamma a kan kasashen biyu.
A na shi bangaren kakakin fadar Krimlin Dmitry Peskov ya ce bangarorin biyu sun tattauna kan matsalolin kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya. Inda shugaban Putin ya bayyana cewa yana goyon bayana a warware matsalar shirin nukliyar kasar ta hanyar tattaunawa.
Kasashen biyu wadanda suke fama da yaki ko kuma wasu matsaloli da kasashen nyamma suna aiki tarem don tabbatar da cewa sun fita daga cikinsu tare da taimakawa juna.
Pekov ya kara da cewa bangarorin biyu sun tattauna batun yadda al-amura suke kara tabarbarewa a kasashen yammacin Asiya.