Mahajjatan Bana Sun Tafi Tsayiwar Arafat A Yau Asabar 9 Ga Watan Zul-Hijjah A Kasa Mai Tsarki

Sama da mahajjata miliyan daya da rabi ne suka kwarara zuwa tsayiwar Arafat domin gudanar da mafi girman rukunnan aikin Hajji A safiyar yau asabar

Sama da mahajjata miliyan daya da rabi ne suka kwarara zuwa tsayiwar Arafat domin gudanar da mafi girman rukunnan aikin Hajji

A safiyar yau asabar 9 ga watan Zul-Hijjah, sama da mahajjata miliyan 1.5 ne suka fara kwarara zuwa filin Arafat domin gudanar da aikin Hajji mafi girma, bayan sun kwana a Mina a ranar Tarwiyah.

Hukumomin Saudiyya sun sanar da zuwan maniyyata fiye da miliyan 1.5 daga kasashen duniya daban-daban, bisa la’akari da karuwar gargadin da hukumomin kasar suka yi dangane da yanayi, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta tabbatar da cewa ana daukar yanayin zafi a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a bana.

A baya, ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Saudiyya ta sanar da kammala jigilar mahajjata daga Makkah da Masallacin Harami zuwa Mina, domin kwana a can a shirye-shiryen zuwa Arafat domin tsayuwar Arafat.

Kakakin ma’aikatar tsaron ya tabbatar da cewa an dauki tsauraran matakan tsaro a kewayen wurare masu tsarki har zuwa karshen ayyukan Hajji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments