Ma’aikatar Tsaron Amurka Ta Pentagon Ta Yi Furuci Da Hasarar Da Harin Iran Ta Janyo Mata

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi furuci da cewa hakika an lalata sansanin sojin saman Amurka na Al Udeid na Qatar Kakakin ma’aikatar tsaron

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi furuci da cewa hakika an lalata sansanin sojin saman Amurka na Al Udeid na Qatar

Kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Sean Parnell ya yi furuci da cewa: Makami mai linzami na Iran da aka kai hari da shi kan sansanin jiragen sama na Al Udeid da ke Qatar, a harin da Iran ta kai a watan Yunin da ya gabata ya janyo barna.

Sanarwar ta Pentagon ta zo ne bayan da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya wallafa hotunan tauraron dan adam da ke nuna irin barnar da harin ya janyo wanda shugaban Amurka Donald Trump ya musanta a lokacin.

A cewar hotunan tauraron dan adam da kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya yi nazari a ranar Juma’a, harin da Iran ta kai kan sansanin Al Udeid da ke Qatar ya yi kamari kuma ya afkawa wani gida mai dauke da kubba mai kusurwa uku da Amurkawa ke amfani da su wajen samun amintattun hanyoyin sadarwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments