Ma’aikatar Shari’a Ta Sojojin Kasar Iran Ta Ce; Dakarun ‘IRGC’ Barkono Ne A Idanun Makiya

Ma’aikatar Shari’a ta Sojin Iran ta jaddada cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci barkono ne a idanun makiya Shugaban hukumar shari’a ta sojojin kasar

Ma’aikatar Shari’a ta Sojin Iran ta jaddada cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci barkono ne a idanun makiya

Shugaban hukumar shari’a ta sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da kuma sauran dakarun kasar sun kare juyin juya halin Musulunci da al’ummar Iran da kuma al’ummar yankin da ake zalunta da dukkan karfinsu tsawon shekaru 47 da suka gabata. A kodayaushe sun kasance barkono ne a idon maƙiyan Musulunci da ƙasa. Hujjatul-Islam Ahmad Pourkhagan ya gana da babban kwamandan Dakarun Juyin Juya halin Musulunci Manjo Janar Mohammad Pakpour a ranar jiya Asabar a yayin bikin tunawa da shahadar kwamandan Dakarun na ‘IRGC’, Laftanar Janar Salami. Ya ce: Duk da cewa rashin shahidi Salami babban rashi ne ga kasar, amma nadin da aka yi ga jajurceccen jagora wajen tafiyar da dakarun rundunar sojin kasa ta ‘IRGC’ da kuma gogewarsa a fagen tsaro mai alfarma da Jagoran juyin juya halin Musulunci cikin kankanin lokaci, ya dakile makircin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke son haifar da hargitsi a cikin kasar.

Hujjatul-Islam Ahmad Pourkhagan ya yi nuni da cewa: Shahidi Salami yana da kyakkyawar hadin kai da bangaren shari’a wajen hana aikata laifuka da tabbatar da doka, kuma sabon kwamandan dalibansa ne, tabbas zai ci gaba da wannan tafarki. Ya kara da cewa, harba makamai masu linzami da al’ummar kasar suka kera da kuma tasirin da suke da shi kan yankunan da aka mamaye na Falasdinawa ya haifar da dagula yakin kwanaki 12 da ya tilastawa makiya amincewa da tsagaita bude wuta.

A nasa bangaren, Manjo Janar Mohammad Pakpour, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), ya nuna jin dadinsa ga shugaban hukumar shari’a ta sojojin kasar a wannan taro, inda ya ce, “Kiyaye lafiya dakarun da lafiyar ma’aikatan IRGC abu ne da ya kamata a sanya a gaba, kamar yadda aka saba a baya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted