Shugaban mabiya darikar Orthodox na kasar Girka na birnin Qudus ya yi kira ga kasashen duniya da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na magance wahalhalun da al’ummar Falasdinu suke ciki a Zirin Gaza, yana mai jaddada cewa: Tilas ne tsagaita bude wuta a matsayin matakin farko na samun zaman lafiya mai dorewa.
Shafin yada labaran Falasdinawa na “Wafa” ya watsa rahoton cewa: Shugaban darikar ta Orthodox a birnin Qudus ya kara da cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, cewa: Dole ne a tsagaita bude wuta a Zirin Gaza, tare da neman samun hakikanin zaman lafiya da ke nuna adalci da kuma kiyaye mutuncin bil’adama.
Ya ci gaba da cewa: “Mummunan tasirin yakin da aka yi a Gaza bai takaita a tarwatsa kayayyakin amfanin bil-Adama ba, amma ya fadada zuwa ga samar da wani mummunan rauni mai zurfi a cikin zukatan duk mai dauke da ruhin dan Adamtaka a fadin duniya, kuma wahalar da al’ummar Gaza suka shiga tana wakiltar raɗaɗi ne a dukkanin zukatan ‘yan Adan wanda ke kira ga aikin gama gari don farfado da ka’idodin. adalci da rahama a tsakanin al’ummun duniya.