Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya ce: Hadin kai da fahimtar juna su ne jajayen layin kasa, kuma babu wanda ke da hakkin ketare su. Ya kuma jaddada cewa tsallaka wannan jan layi na nuni da wuce gona da iri ga tsarin mulki. Ayatullah Khatami ya ci gaba da cewa a yau daga mumbarin sallar Juma’a a birnin Tehran na kasar Iran cewa: Hadin kai da fahimtar juna suna daga cikin umarnin alkur’ani mai girma da kuma sakon da Imam Khumaini (Allah ya yi masa rahama) da Jagoran juyin juya halin Musulunci a kodayaushe suke jaddadawa.
Ya kuma yi gargadi kan haifar da rarrabuwar kawuna da sabani a tsakanin al’umma, yana mai cewa al’ummar Iran sun isar da sakon tsayin daka ga duniya a tsawon kwanaki 12 da aka shafe ana yakar kasar.
Ya kara da cewa: Wasu mutane suna ta maimaita kalaman karfin Amurka da gwamnatin ‘yan sahayoniyya a daidai lokacin da Amurka da wannan gwamnatin ‘yar mamaya ke ganin duk mafarkinsu ya ruguje.
Ya ci gaba da cewa: Makamashin nukiliya shi ne makamashin makomar duniya nan gaba. Karfin burbushin halittu yana gab da bacewa kuma zai bace. Yayin da bunkasa harkar noma, wutar lantarki, ruwa, da sauran muhimman bukatun kasa za sui dogara a kan makamashin nukiliya.