Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Juma’a A Tehran Ya Ce: Matsin Lamba Kan Iran Bai Yi Tasiri Ba

Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Karin matsin lamba daga makiya yana kara Iran juriya da jajurcewa Limamin da

Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya jaddada cewa: Karin matsin lamba daga makiya yana kara Iran juriya da jajurcewa

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Hujjatul-Islam Kazem Siddiqi ya yi nuni da irin nasarorin da gwamnatin Musulunci ta Iran samu wajen fuskantar takunkuman zalunci da aka kakaba mata, yana mai jaddada cewa: Iran ta hanyar dogaro da karfin cikin gida, gudanar da ingantattun tsare-tsare, da zurfafa tunani cikin tsanaki, zata iya shawo kan matsalolin da take fuskanta daga makiya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya watsa rahoton cewa: A cikin hudubar tasa a wannan mako, Hujjatul-Islam Siddiqi ya tabo jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci dangane da Jihadin Fadakarwa da kuma kalubalantar makirce-makircen makiya, yana mai nuni da hanyoyin makiya na haifar da sabani da raunana hadin kan kasa.

Yana mai bayyana cewa: Makiya na amfani da manyan makamai guda uku da suka hada da:- Rusa karfin zukatan al’umma, da yada tsoro a tsakaninsu, da kuma kunna wutar sabani da fitina a tsakaninsu ta hanyar yada jita-jita da karairayi, har su yi nasarar janyo rarraubuwar kawuna tsakanin al’umma da gwamnati don samun damar cimma munanan manufofinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments