Likitocin Iran Suna Ci Gaba Da Samun Nasara Wajen Magance Matsalar Kurmanta Da Na Bebantaka

Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin

Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar

Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa a yayin bikin nasarar da aka yi na aikin tiyatar dashen na’urar magance matsalar Rashin ji da rauninsa sau 1,500 a lardin Khuzestan dake kudu maso yammacin ƙasar. Wadannan tiyata sun bayyana kwarewar aikin likita da basirar likitoci a lardin, wajen maido da ji da magana ga wadanda suka rasa jin tun da fari.

Bikin dai ya samu halartar likitoci da ma’aikatan jinya da yara da dama wadanda aka yi musu aikin tiyata cikin nasara, tiyatar da ta ba su damar bayyana tunaninsu da yadda suke ji a fagen rayuwa.

Hanyoyin dasa na’urar a lardin sun zama wani dandamali mai karfi ga marasa lafiya na kasashen waje, inda marasa lafiya 36 daga kasashen Iraki, Oman, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkey da Afghanistan suka samu waɗannan ni’imomi a fagen rayuwar bil-Adama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments