Search
Close this search box.

Likitocin Amurka Sun Fice Daga Gaza Saboda Laifukan Da Aka Tafkawa Kan Falasdinawa

Likitocin Amurka da suka dawo daga Gaza sun ba da labarin munanan al’amuran kisan kiyashi a yankin! Wasu gungun likitocin da suka dawo daga Zirin

Likitocin Amurka da suka dawo daga Gaza sun ba da labarin munanan al’amuran kisan kiyashi a yankin!

Wasu gungun likitocin da suka dawo daga Zirin Gaza na Falasdinu kwanan nan sun yi kira ga shugaban Amurka Joe Biden da gwamnatinsa da su gaggauta kakabawa gwamnatin yahudawan sahayoniyya takunkumin makamai.

Wannan ya zo ne a wani taron manema labarai da likitocin Amurka da ke halartar babban taron jam’iyyar Democrat da aka gudanar a jihar Chicago.

Likitocin sun bayyana cewa hare-haren na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun lalata Gaza, kuma idan Amurka ba ta kakaba wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila takunkumin hana mallakar makamai cikin gaggawa ba, to za ta ci gaba da zama abokiyar huldar ta da aikata laifuka.

Tami Abu Ghanem, daya daga cikin likitocin da suka fito daga Gaza, ya ce hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa na tsawon watanni 10 sun sanya rayuwar fararen hula a Gaza ba zata yiwu ba.

Ya kara da cewa: Ba za su iya yin aikinsu ba yayin da bama-bamai ke fadowa, kuma ‘yan sari-ka-noke na haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan kananan yara da fararen hula, sannan jirage masu saukar ungulu na yahudawan sahayoniyya suna sauka a kan gungun fararen hula, saboda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanya aikin ceto ba zai yiwu ba tare da taimakon Amurka kai tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments