Lebanon Tana Bukatar Sakin Yan Siriya Da Suke Gidajen Yarin Kasar Kasar Zuwa gwamnatin kasarsu

Gwamnatin kasar Lebanon tana bukatar ta cimma yarjeniya da gwamnatin kasar Siriya saboda rage yawan fursinoni na kasar Siriya wadanda suke tsare a cikin gidajen

Gwamnatin kasar Lebanon tana bukatar ta cimma yarjeniya da gwamnatin kasar Siriya saboda rage yawan fursinoni na kasar Siriya wadanda suke tsare a cikin gidajen yarin Lebanon da suka cika.

Jaridar ther nation ta kasar Amurka ta ce zata idan gwamnatin kasar Siriya tana son su karasa kason nasu a gidajen yarin kasar. Labarin ya kara da cewa gidan yarin Roumieh na kasar ta Lebanon ta farfado da kotu wacce zata gaggauta yanke hukunci kan wadanda suke jiran sharia don rage cinkoso a gidajen yarin kasar, Kotun dai ya yi aiki irin wannan a lokacin Cutar Covit 19 don rage cinkoso a gidajen yarin kasar musamman don fitar da yan kasashen waje daga cikin gidajen yarin.

Ministan sharia a na kasar Lebanon Adel Nassar ne ya kawo wannan shawarar bayan kafa sabuwar gwamnati a kasar ta Lebanon a farko wannan shekarar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments