Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil).
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ne ta shigar da ƙarar gaban membobi 15 na kwamitiin Tsaron.
Labanon ta yi kira ga kwamitin Tsaro da Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya da su ɗauki matakan gaggawa don hana Isra’ila keta hurumin Lebanon.
A cewar ƙarar, keta hurumin ya kunshi gina katanga biyu da Isra’ila ta yi a kudu maso yamma da kudu maso gabashin Yaroun, a cikin iyakokin Lebanon da aka amince da su a duniya.
Gina wadannan katanga ya kunshi kwace wani bangare na Lebanon kuma ya zama keta Kudurin kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701 da yarjejeniyar tsagaita wuta ta 2024, ta tanada in ji sanarwar.
Tawagar MDD a yankin wato UNIFIL ta bukaci Kwamitin Tsaro da ya tilasta wa Isra’ila ta rushe katangar biyu tare da tabbatar da cewa ta janye nan take daga kudu da Layin Shuɗi daga duk yankunan da har yanzu take mamaye da su a Lebanon, gami da mashigar kan iyaka guda biyar.