Kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta bada sanarwan cilla makamai masu linzami samfurin katusha kan taron sojojin yahudawa a wasu gidaje yankin Galili na kasar Falasdinu da aka mamaye, wanda aka fi saninsa da yankin shekara 1948.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanan da kungiyar ta fitar dangane da wadannan hare hare na cewa, sun kai wadannan hare hare ne don tallafawa Falasdinawa a yankin gaza, wadanda sojojin yahudawan suke wa kisan kare dangi, sannan da kuma maida martani kan kashe wani dan kungiyar wanda jiragen yakin HKI suka yi a kudancin kasar.
Muhammad Farraan ya yi shahada ne a garin Nabatiyya na kudan cin kasar ta Lebanon, sannan wasu yan makaranta suka ji raunuka a lokacinda jiragen yakin HKI suka kai hare hare a kan garin.
Majiyar sojojin yahudawan ta bayyana cewa Muhammad Farraan yana daga cikin mayakan kungiyar Hizbullah wadanda suke kera makamaiwa kungiyar.
A wata sanarwan kungiyar tace ta kai hare hare kan tankar yaki samfurin Mirkava mallakin sojojin HKI a dajin Shtula tare da amfani da makaman tarwatsa tankunan yaki samfurin ATGM, wanda ya tawatsa tankar ya kula halaka ko raunata sojojin da ke cikinsa.
A kasar Iraki kuma dakaru masu gwagwarmaya day an ta’adda sun bada sanarwan a shafinsu na Telegram kan cewa sun kai hare hare kan waurare masu muhimmanci da dama a HKI. Labarin ya kara da cewa dakarun na kasar Iraki sun kai hare hare kan garin Haifa nab akin ruwa tare da amfani da makaman dron masu kunban bakin wake. Banda haka sun kai wasu hare haren da irin wadannan makamai kan yankunan arewa maso yammacin kasar Falasdinu da aka mamaye.
Daga karshen labarin ya kammala da cewa sun kai hare haren ne don tallafawa falasdinawa wadanda sojojin HKI suke wa kisan kare dange a yankin gaza.