Lavrov : Rasha a shirye take ta taka rawa a shiga tsakanin Amurka a Iran

Kasar Rasha ta ce a shirye ta ke ta taka rawa a shiga tsakani game da boyayiyar ajandar Amurka game da Iran. Ministan Harkokin Wajen

Kasar Rasha ta ce a shirye ta ke ta taka rawa a shiga tsakani game da boyayiyar ajandar Amurka game da Iran.

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana cewa Moscow ta taka muhimmiyar rawa a ƙarshen yarjejeniyar nukiliya ta Iran  ta 2015, ya ƙara da cewa ɓangarorin Iran, Amurka, da Isra’ila sun san cewa Rasha a shirye take ta shiga tsakani da kuma aiwatar da irin wannan tsari.

Lavrov ya jaddada cewa Rasha za ta yi farin cikin taimakawa wajen hana ƙarin tashin hankali, kamar wanda ya faru a watan Yunin 2025, lokacin da aka jefa bama-bamai a cibiyoyin nukiliyar Iran da ke ƙarƙashin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA).

Ya ci gaba da nuna cewa, IAEA ba ta fitar da wata sanarwa da ke Allah wadai da wannan keta ƙa’idarta da Yarjejeniyar hana yaɗuwar Makamai Nukiliya (NPT) ba

Da yake magana game da kalaman Donald Trump da barazanar da ya yi wa Iran, Ministan Harkokin Wajen Rasha ya ce, “Ina fatan hankali zai yi nasara.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted