Babban sakataren majalisar koli ta tsaron jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Za a bunkasa aiki tare a tsakanin Iran da Saudiyya a fagagen tattalin arziki da kuma tsaro.
Dr. Larijani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowar daga ganawar da ya yi da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman.
Bugu da kari Dr. Ali Larijani ya ce a yayin ganawarwa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad Bin Salman, sun tattauna hanyoyin bunkasa alakar kasashensu ta fuskoki mabanbanta, da kara girman wannan alakar ta fuskar tattalin arzki da tsaro fiye da yadda take a yanzu.”
Haka nan kuma ya ce, za a yi aiki domin kawar da dukkanin abubuwan da suke kawo cikas a kan hanyar bunkasa wannan alakokin.
Dr. Ali Larijani ya kuma ce,an yi shawara akan yadda kasashen yankin za su bunkasa alakarsu ta tsaro domin ganin an tabbatar da zaman lafiya.
Da aka tambaye shi akan ko an sami sauyi akan mahangar kasashen Larabawa bayan harin da HKI ta kai wa Qatar, Dr.Ali Larijani ya ce; Tabbas da akwai sauyi a cikin yadda kasashen larabawa suke Kallon abubuwan da suke faruwa, domin suna ganin cewa kasantuwar HKI a cikin wannan yankin yana hana zaman lafiya.
Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ziyarci Saudiyya inda ya gana da ministan tsaronta da kuma Yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman.