Search
Close this search box.

Landan: Daliban Jami’ar Queen Mary sun shiga gangami don nuna goyon baya ga al’ummar Gaza

A ci gaba da nuna goyon baya ga al’ummar zirin Gaza, daliban jami’ar Queen Mary da ke birnin Landan sun kafa sansani tare da neman

A ci gaba da nuna goyon baya ga al’ummar zirin Gaza, daliban jami’ar Queen Mary da ke birnin Landan sun kafa sansani tare da neman a janye duk wasu yarjeniyoyi na jami’ar gaba daya daga kamfanoni masu alaka da “Isra’ila”.

A wajen babban ginin jami’ar , an kafa tantuna da dama, kuma filin ya cika makil da dalibai kafin daga bisani kuma jama’ar gari da ke kusa da wuri su ma suka shiga.

Masu zanga-zangar, dalibai ne da sauran ‘yan kasa, inda suka yi ta rera taken “Dakatar da kai hari kan Falasdinu”, “Dakatar da mika makamai ga Isra’ila”, da kira a dakatar da Isra’ila daga yin kisan kare dangi a Rafah.”

A cewar kamfanin dillancin labarai na Andalou, wani dalibi ya ce, “Ba mu ji dadin yadda gwamnatinmu take nuna halin ko in kulak an ayyukan kisan kiyashin da Isra’ila take yi wa fararen hula a Gaza, da kuma yadda gwamnatin Burtaniya take baiwa Isra’ila makamai da ake yin amfani da su wajen aikata wannan babban laifi na yaki, saboda haka Mun yanke shawarar cewa ya isa,” ya kara da cewa ” Dukanmu muna nuna alhini kan ga al’ummar Falastinu, domin mun san cewa muna yin abin da ya dace ko da kuwa an hukunta mu, har yanzu akwai lamiri na ‘yan adamtaka tare da mu wajen da yin tsayin daka kan abin da ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments