Kwamitin kungiyoyin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa ya tabbatar da cewa: Kalaman ministan tsaron Isra’ila Katz game da “bude kofofin jahannama” kan birnin Gaza ya zama kira ga jama’a na Aiwatar da kisan kiyashi, kawar da wata al’umma daga kan doron kasa da kuma kai hare-haren wuce gona da iri kan ababen more rayuwa da farare hula.
Kwamitocin sun bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa: Laifukan da sojojin mamaya Isra’ila suka aikata a birnin Gaza, da suka hada da barna, ta’addanci, da kuma kashe jama’a, sun bayyana hakikanin fuskar “hukumar da ke karkashin jagorancin ‘yan ta’adda marasa tunanai kuma masu tsattsauran ra’ayi,” wadanda ke ci gaba da aikata manufofinsu na kisan kiyashi kan fararen hular da ba su da kariya bisa hujjar karya bayyananniya.
Sun yi nuni da cewa harin da aka kai kan hasumiyoyi da kuma ci gaba da rugujewar tsari ba zai iya faruwa ba in ba tare da goyon baya da cikakkiyar karfafawa, da kuma tsoma bakin gwamnatin Amurka ba, wanda ta fito fili tana bayyana matsayinta na daukar nauyin ta’addancin yahudawan sahayoniyya.”