Kwamitin tsaro na MMD zai gudanar da taron gaggawa a cikin yan kwanaki masu zuwa don tattauna batun munanan hare haren da sojojin HKI suke kaiwa a garin Rafah na kudancin zirin gaza.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar majalisar tana fadar haka a jiya, sannan ta kara da cewa gwamnatin kasar Aljeriya ce ta bukaci wannan zaman gaggawa.
Kafin haka dai, wani babban jami’i a kwamitin tsaro ya bayyanawa kamafanin dillancin labaran ITAR-TASS na kasar Rasha kan cewa, sojojin HKI sun kai mummunan hare hare a kan sansanin yan gudun hijira a garin Rafah, inda ta cilla makamai masu linzami masu kuma karfi har guda 8 kan sansanin yan gudun hijira.
Hare haren dai sun yi sanadiyyar tashin gobara a kan haimomin yan gudun hijirar, ya zuwa yanzi kimani mutane 50 ne suke konme kurmus a wannan harin. Sannan wasu da dama suka ji rauni.
Gwamnatin kasar Aljeriya c eta bukaci a gudanar da taron ba tare da yan jirada ba, don tattauna wannan batun da kuma yadda za’a kawo karshen yakin.
Kafin haka dai babban sakataren MDD Antonio Gutteres ya bayyana cewa babu wani wuri tudun na tsari a gaza.
Kungiyar bada agaji ta ‘Action Aid’ ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa sansanin yan gudun hijira a Rafa wanda sojojin HKI suka cillawa makamai a jiya litinin, yakamata ya zama tudun na tsirane ga falasdinawa fararen hula musamman mata da yara. Mafi yawan wadanda sojojin sojke kashewa mata da yara ne.