Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gana cikin gaggawa a wannan Litinin domin tattauna halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.
Kwamitin zai gana cikin gaggawa bisa bukatar Iran domin tattauna halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda fadar shugaban kasar Switzerland ta sanar.
Kasashen Aljeriya, China da Rasha, duk sun goyi bayan bukatar da Iran din ta gabatar biyo bayan harin Isra’ila kan kasar a ranar Asabar.
Babban jami’an diflomasiyyar Iran ya bukaci kwamitin sulhu na MDD, da da ya yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A nasa bangare Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce mahukuntan kasar ne ke da alhakin yanke hukunci kan irin yadda Iran za ta nuna karfinta ga gwamnatin Isra’ila.
Ayatullah Khamenei ya ce kamata ya yi a dakile kuskuren lissafin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi kan Iran.
Shi kuwa shugaban kasar ta Iran, Masoud Pezeshkian, cewa ya yi, kasarsa bata neman yaki, amma za ta maida ” martanin da ya dace ‘ ga harin Isra’ilar na ranar Asabar.