Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran ya bayyana cewa: Sabbin barazanar da ake yi wa Iran za su fuskanci sabbin mayar da martani
Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran Birgediya Janar Keumarth Heydari ya bayyana cewa: Sabbin barazanar da ake yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran lallai za su fuskanci sabbin mayar da martani masu gauni, yana mai jaddada cewa: Sojojin Iran bisa karfi da dogaro da kansu, sun ba da himma a fagen samar da makaman kariya da ruhin sadaukarwa don daukar matakan da suka dace da irin barazanar da suke tunkarar kasarsu da kuma ci gaba da kasancewarta kasa daya dunkulalliya.
Wannan ya zo ne a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Haidari ya fitar a gefen kaddamar da ayyukan samar da manyan bindigogi 33mm da makamai masu linzami kirar Sahand 3. Ya kuma jaddada cewa: Wadannan nasarori biyu da Iran ta samu a fagen kira makamai zasu taimaka a wajen kara shirye-shiryen da rundunar sojin kasa suke yi domin tsarin tsaron kasa.