Janar Salami wanda shi ne kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ya aike wad a babban magatakardar kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hizbullah sakon ta’aziyyar shahadar Abu Muhsin,Fu’ad Shukur.
Janar Salami ya bayyana shahadar ta Fu’ad Shukur da cewa; makiya su saurari mayar da martani mai tsanani daga muminai da ‘yan gwgawarmaya.
Da daren ranar Talata ne dai ranar 23 ga watan Yuli HKI ta kai hari akan wani gini dake unguar Dhahiyal-Junubiyyah a birnin Beirut wanda ya yi sanadin shahadar Fu’ad Shukur da daya ne daga cikin kwamandajojin kungiyar ta Hizbullah.