Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Wadanda suka sha kashi a Gaza da Lebanon su ne jagororin kai hari a kasar Siriya
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Manjo Janar Hussein Salami ya jaddada cewa: ‘Yan ta’adda masu kafirta musulmi karkashin jagorancin wadanda aka fatattake su a fagen yaki a Gaza da Lebanon sune ke jagorantar munanan hare-hare a kan kasar Siriya.
A sanarwar da ya fitar Manjo Janar Salami ya bayyana alhininsa dangane da shahadar mai ba da shawara kan harkokin soji na Iran, Birgediya Janar Kayomarth (Hashem) Pourhashemi, a garin Halab na kasar Siriya a hannun kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi. Manjo Janar Salami ya ci gaba da cewa: Tare da ire-iren rugujewan muggan tsare-tsaren yahudawan sahayoniyya a fagen yaki a Zirin Gaza da Lebanon, da rashin cimma munanan manufofinsu a kan kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci, yanzu sun dawo ta hanyar ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi don cimma wasu munanan bukatunsu na sharri, inda suka ingiza gungun’yan ta’adda suka kai munanan hare-hare kan kasar Siriya a karkashin ajandarsu da suka tsara a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, amma duk da haka sun fuskanci mayar da martani daga sojoji da dakarun farin kaya na wannan kasa.