Kwamandan Dakarun Juyin Juya Hali ya bayyana ewa: A shirye suke su sake kai munanan hare-hare kan abokan gaba
A yayin ganawarsa da kwamandan sojojin Iran, Manjo Janar Hatami, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada shirin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na IRGC na sake kai farmaki kan makiya. Ya ce: “Ba za su kyale masu wuce cgona da iri ba, kuma za su ci gaba da yaki da makiya tun daga inda suka tsaya.
A yayin taron, Manjo Janar Pakpour ya jaddada cewa: Kwarjinin dqkarun jkare juyin juya halin Musulunci yana kan mataki madaukaki, yana mai bayyana cewa; Dakarun kasar na cikin cikakken shiri da hadin gwiwar sake tunkarar duk wani farmaki daga makiya.
Manjo Janar Pakpour, ya fara jawabinsa ne da tunawa da shahidan Masu girma musamman Manjo Janar Mohammad Baqiri, Manjo Janar Hossein Salami, Manjo Janar Gholam Ali Rashid, da Manjo Janar Ali Shadmani.
Jagoran ya yaba da irin bajintar da al’ummar Iran suka nuna a lokacin da ake gudanar da bukukuwan kare alfarma na kwanaki 12, bisa da la’akari da tsayin dakan da al’ummar Iran suka yi a matsayin mafi muhimmanci da kuma goyon bayan da suke baiwa sojojin kasar, yana mai cewa “Hadin kai a adadi” shi ne mafaka mafi karfi na kasar Iran. Dakarun Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun dakile yaki da makirci mafi hadari da sarkakiya a tarihi a kan Iran tare da goyon bayan al’umma.