Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa da dama sun bayyana bacin ransu kan barazanar da ministan yakin Isra’ila ya yi na bude “kofofin jahannama” a zirin Gaza.
Wannan martanin ya zo ne a ranar Juma’a bayan da Isra’ila Katz ya ayyana cewa gwamnatin sahyoniyawan na gab da maida yankin jahannama a gabar tekun.
Katz, ya bayyana cewa sojojin Isra’ila za su zafafa kai hare-hare har sai kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta sako mutanen da aka kama.
A nata bangaren, Hamas ta ayyana barazanar Katz a matsayin “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba ga dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai.”
Kalaman na Katz na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta riga ta ba da damammaki don ba da damar sakin mutanen da aka kama da kuma kawo karshen yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza, wanda ya fara a watan Oktoban 2023, amma gwamnatin Tel Aviv ta ki amincewa da wannan rangwame.
Kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu, ita ma ta yi tsokaci kan kalaman Katz game da harin bama-bamai da sojoji suka yi kan gidaje, tana mai cewa wadannan kalamai laifukan yaki ne.”
A nasu bangaren, kwamitocin Resistance Popular, sun jaddada cewa, ikirarin da Katz ya yi dangane da tsanantar ta’addancin da ake yi a zirin Gaza, kira ne a fili na kisan kiyashi da kawar da wata kabila.