Kungiyoyin Duniya Zasu Yi Gangamin Goyon Bayan Falasdinu

Kungiyoyi 200 a ƙasashe 60 suna shirya wani gangami na duniya ga Falasɗinu. Kungiyar Kawancen Duniya don Falasdinu (GAFP), tare da goyon bayan Kungiyar Kawancen

Kungiyoyi 200 a ƙasashe 60 suna shirya wani gangami na duniya ga Falasɗinu.

Kungiyar Kawancen Duniya don Falasdinu (GAFP), tare da goyon bayan Kungiyar Kawancen Yaki da Wariyar launin fata (AAM) da kuma Kungiyar Kawancen Duniya da ke Yaki da Mallakar Falasdinu (SAND), sun yi kira ga kungiyoyin fararen hula, kungiyoyin kwadago, kungiyoyin dalibai, da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam da su shirya tarurruka a fadin nahiyoyi shida.

A cewar wata sanarwa daga kungiyar, matakin na da nufin neman a dauki alhakin laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil’adama, aiwatar da dokokin kasa da kasa, da kuma takaita sayar da makamai ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Taron zai dauki nau’o’i daban-daban, ciki har da zanga-zanga, zaman dirshan, da ayyukan al’adu da ilimi a birane kamar London, Sydney, Cape Town, São Paulo, Rabat, Quito, Mexico City, Istanbul, Santiago, Reykjavik, Bangkok, Athens, da Kuala Lumpur.

Kungiyoyin da suka shiga taron kuma suna da niyyar kalubalantar hukumomin gwamnati da na kasuwanci da ke da alaƙa da hanyoyin samar da kayan aikin soja ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted