Kungiyoyi a faransa sun sake fitowa a wata zanga zanga yau Asabar a faransa.
Wannan ita ce Asabar ta hudu a jere da kungiyoyi ke fitowa kan tituna a fadin kasar ta faransa, kan tsadar rayuwa, hauhawan farashin makamashi da kuma neman inganta yanayin ilimi ga matasa.
Ƙungiyoyin kwadago, daliban makarantun sakandare, daliban jami’a, da ‘yan zanga zangar da ake wa lakabi da ”Jillet jaune” sun kira jama’a da su sake fitowa kan tituna, kwana biyu bayan babban gangamin ranar Alhamis, 5 ga wata wanda ya hada mutane kimanin 600,000 (a cewar hukumomi).
A nata bangare Kungiyar Kwadigo ta kasar CGT, ta kiyasta mutum miliyan 1.6 da suka shiga zanga zangar ta ranar Alhamis data gabata a faɗin kasar.
A birnin Paris, kungiyar kungiyoyin kwadago da kungiyoyin matasa za su bi hanya daya kama ranar Alhamis, daga dandalin ”Place de la République” zuwa dandalin ”Place de la Nation”.
Ƙungiyoyin kwadago sun yi gargadin cewa za su ci gaba da kasancewa cikin shirin har sai gwamnati ta magance koke-koken su, musamman game da tsadar rayuwa.
A yanzu haka, suna jiran zaman da FiraMinistan kasar Sébastien Lecornu zai yi a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba.
Kungiyoyin daio sun ce kara karamin albashi, wanda aka riga aka ambata, ba zai isa ba.