Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya nada Tracey Ann Jacobson a matsayin jakadiyar Amurka a birin Bagdaza na kasar Iraki, inda hakan ya fusata wasu kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar, sun kuma bukaci gwamnatin kasar ta dauki mataki a kanta.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wadanda suka san Jacobson sun bayyana irin mummunan munufofinta ga mutanen kasar Iraki. Daga ciki ta bayyanwa majalisar dattawan Amurka kan cewa, matsalar kasar iraki it ace samuwar wadannan kungiyoyi wadanda suke yaki Daesh a kasar.
Ta kuma kara da cewa Iraki ba zata sami zaman lafiya ba matukar wadannan kungiyoyin suna nan. Amma kungiyar Kata’ib Hizbulla da sauran kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar sun ja kunnen gwamnatin kasar Iraki dangane da halayen Jaconson, kuma sun bukaceta ta magance matsalar da sauri, don idan bata yi haka ba, suna iya daukar matakan da suka dace a kanta.
Abu Ali al-Askari shugaban kungiyar Kata’ib Hizbullah ya bayyana cewa samuwar sojojin kasar Amurka a Iraki shi ne matsala mafi girma ga mutanen kasar Iraki. Sunce matukar sojojin Amurka suna kasar Iraki kasar ba zata taba samun zaman lafiya ba.