Kungiyar Kwadago Ta Yi Watsi Da Kudin Mota N70,000

Kungiyar kwadago ta TUC ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayyar Najeriya na bawa ma’aikata N70,000 a matsayin kudin mota saboda tsadar rayuwan da ake

Kungiyar kwadago ta TUC ta yi watsi da shirin gwamnatin tarayyar Najeriya na bawa ma’aikata N70,000 a matsayin kudin mota saboda tsadar rayuwan da ake fama da shi a klasar.

Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto shugaban kungiyar Festus Osifo yana fadar haka a yau Laraba bayan taron da shuwagabannin kungiyar suka gudanar.

A jiya talata ce Jami’an gwamnatin tarayyar Najeriya suka zauna da shuwagabannin kungiyar inda ta amince ta bawa ma’aikata N70,000 a matsayin kudin mota, wanda zai fara daga watan nuwamba mai kamawa. Sannan zata  biya ma’aikatan bashin kudaden da suke binta tun watan Mayun da ya gabata.

Shugaban kungiyar ta TUC ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara albashin ma’aikata don abinda ake basu a halin yanzu baya isarsu. Ya kuma kara da cewa, hatta karin al-bashin da ta yiwa ma’aikatan a shekara ta 2023 bai gama dukkan ma’aikatan gwamnatin tarayyar ba. Ya ce tsoronsu shi ne gwamnatin tarayyar bata cika alkawalin da suka cimma da ita a baya ba, ta yaya zasu amince da sabbin alkawula. ? ya ce kashi 80% na gwamnatocin jihohin kasar basu aiwatar da karin da aka yiwa ma’aikata a baya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted