Kungiyar Kwadago Ta Tunusiya Za Ta Shiga Yajin Aiki Na Gama-Gari A Duk Fadin Kasar

Kungiyar kwadago mafi girma ta kasar Tunusiya ta yanke shawarar shiga yajin aikin gama-gari tare da kauracewa zaben kasar Kungiyar kwadago ta kasar Tunusiya ta

Kungiyar kwadago mafi girma ta kasar Tunusiya ta yanke shawarar shiga yajin aikin gama-gari tare da kauracewa zaben kasar

Kungiyar kwadago ta kasar Tunusiya ta gudanar da zamanta na kasa a birnin Monastir, ta yanke shawarar fara gudanar da yajin aikin gama-gari a duk fadin kasar, wanda za ta tantance ranar da za a fara shi nan gaba, da kuma aniyarta ta kauracewa zaben shugaban kasa da ke tafe a kasar.

An dai amince da matakin ne a cikin kudurorin da majalisar kungiyar ta kwadago ta yanke, kuma daga baya majalisar zartaswa ta kasa za ta tantance ranar da za a fara yajin aikin da ya hada da kamfanoni masu zaman kansu da ma’aikatun gwamnati da kuma kauracewa ayyukan gama gari a kasar.

Sakatare-Janar na Kungiyar Kwadago ta Tunisiya, Nouruddine Taboubi, ya nemi afuwa a jawabinsa na ranar karshe ta zaman Majalisar zartaswar a birnin Monastir kan sake fasalin babi na 20, kuma yana ganin kuskure ne wanda ya dauki cikakken alhakinsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments