Daya daga cikin Jagororin kungiyar Jihadul-Islami ya ce: Sansanonin ‘yan gudun hijiran Falasdinawa sun zame abin tsoro ga ‘yan mamaya
Daya daga cikin jagororin kungiyar Jihadul-Islami Mahfouz Munawar ya tabbatar da cewa: Sansanonin ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suke gabar yammacin kogin Jordan sun zame wasu wuraren abin tsoro ga sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai nuni da cewa ci gaba da kai hare-haren wuce gona da irin sojojin yahudawan sahayoniyya kan yankin gabar yammacin kogin Jordan ba su da bambancin irin kisan kiyashin da ake kai wa kan yankin Zirin Gaza.
Munawar ya bayyana haka ne a hirar da ya yi da tashar Al-Hadath inda ya ce: Abin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa a yankunan gabar yammacin kogin Jordan baya da bambanci da abin da ke faruwa a Zirin Gaza, sannan kuma suna kokarin juya akalar yakin da suke yi a Gaza zuwa yankunan gabar yammacin kogin Jordan saboda matsayin da gabar yammacin kogin Jordan ke da shi, saboda a yau ana daukar yankunan a matsayin yankuna da suke hulda kai tsaye da ‘yan mamayar, kuma wuri mafi cin rai ga makiya.