Kungiyar Jihadul-Islami ta yi kira ga hukumar Falasdinu da ta dakatar da yakin da take yi kan Falasdinawa tare da dage matakan killace Jenin da ta yi
Kungiyar Jihadul- Islami ta jaddada cewa: Ba za ta shiga cikin rikicin cikin gida ba, bisa la’akari da farmakin da jami’an tsaron hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Falastinu ke kaddamarwa a sansanin Jenin, tana mai kira ga kungiyar Fatah da ta mayar da hankalinta kan matakan samar da hadin kai tsakanin al’ummar Falasdinu.
Kungiyar Jihadul-Islami ta jaddada cewa: Ba za ta shiga cikin rikicin cikin gida ba, duk da farmakin da jami’an tsaron hukumar Falasdinawa take kai wa kan Falasdinawa a sansanin Jenin.
A cikin wannan yanayi, kungiyar Jihadul-Islami ta yi kira ga kungiyar Fatah da ta mayar da hankali kan batun hadin kan Falasdinawa tare da jaddada yin kira ga hukumar ta Falasdinu da ta gaggauta dakatar da kaddamar da farmaki kan al’ummarta a sansanin Jenin.