Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Lebanon ta zafafa kai hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila lamarin da ya janyo tashin gobara a yankin Galili na yahudawan sahayoniyya
Ana ci gaba da samu bullar musayar wuta tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila a ‘yan kwanakin nan, bayan kisan gillar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi wa wani babban jigo a kungiyar Hizbullahi, inda rahotonni suka bayyana cewa: ‘Yan gwagwarmayar Hizbullahi sun kara zafafa kai hare-hare kan wurare da tarukan sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suke yankunan Arewaci da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Zirin Gaza da kuma mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin ‘yan mamaya.
A safiyar Lahadin, an yi ta jin karar harbe-harbe a yankin karamar hukumar Galilee, kuma an ji karar fashewar wasu abubuwa sakamakon wani babban makami mai linzami da kungiyar Hizbullah ta harba, yayin da hayaki ya turnuke yankin.
Gidan rediyon sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ya watsa rahoton cewa: An yi ta jin karar sautin kararrawar neman yahudawan sahayoniyya su shiga maboyar karkashin kasa a yankunan karamar hukumar Galilee a karon farko tun daga watan Oktoba, ranar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta fara kaddamar da yaki kan Zirin Gaza.