Kungiyar Hizbullah Tana Cigaba Da Kai Wa  HKI Hare-hare

A yau Talata kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hari akan sansanin bayar da horo ga rundunar HKI ta ‘yan sama jannati” dake a matsugunin

A yau Talata kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hari akan sansanin bayar da horo ga rundunar HKI ta ‘yan sama jannati” dake a matsugunin ‘yan share wuri zauna na “ Karma’il”. Hizbullah ta ce, ta yi amfani da makamai masu linzami wajen kai harin.

Bugu da kari kungiyar ta Hizbullah ta sanar da cewa; Da misalin karfe 10;00 na safe ta kai hari da makamai masu linzami da dama akan garin Safad, kuma adaidai wannan lokacin ta kai wani harin akan matsugunin ‘yan share wuri zauna na ‘al-manarah’ da kuma “Kafar Balum”.

Da misalin karfe;11;00 dakarun na Hizbullah sun kai wani harin a kan matsugunin ‘yan share wuri zauna na Avavim  ta hanyar amfani da makamai masu linzami.

A jiya Litinin ma dai kungiyar ta Hizbullah ta kai hare-hare masu tsanani akan sansanoni mabanbanta da su ka hada Akka, Nahariya da kuma birnin Tel Aviv.

Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa; A harin na jiya a birnin Tel Aviv, dan share wuri zauna daya ya halaka yayin da wasu 4 su ka jikkata.

Bugu da kari harin na jiya ya yi sanadiyyar yankewar wutar lantarki a cikin wasu unguwanni na birnin Tel Aviv.

A gefe daya HKI ta bayyana cewa sojojinta 11 sun jikkata a kudancin Lebanon a cikin sa’oi 24 da su ka gabata. Bugu da kari sanarwar ta ce, tun daga fara kokarin shiga kasar Lebanon ta kasa, sojoji 1000 ne su ka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments