Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yada hotunan bidiyo wadanda jirgin leken asirin kungiyar wato ‘Hudhuda’ ya dauka a yankunan tudda Golan na kasar Siriya, inda suke nuna warare masu muhimmanci na sojojin HKI har 17 a cikinsu.
Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta bayyana cewa hutunan sun nuna dukkan miuhimman wurare na leken asiri da sansnonin sojoji da wuraren da suka girka garkuwan makamai masu linzami da sauransu.
Wannan shi ne bidiyo kasha na biyu wanda kungiyar ta yada a jiya Talata, kuma hakan ya kara sanya shuwagabannin yahudawan Sahyoniyya cikin dimwa, saboda yadda kungiyar Hizbulla take da cikekken asiranta na tsaro. Kuma sun tabbatar da cewa tana da karfin wargazasu a duk lokacinda take da damar yin hakan.
Shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa hotunan bidiyo wadanda jirgin leken asirinta ya dauka a kan HKI yafi awa guda ko kuma na awowi ne.
Wannan sako ne ga makiya da masoya inji Muhammad Afif ,jami’in watsa labarain na kungiyar a birnin Beirut na kasar Lebanon.