Search
Close this search box.

Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hare Hare Masu tsanani Kan HKI A Ranaku Biyu A Jere

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a ci gaba da maida martani kan HKI a yau Asabar ma ta kai hare hare masu tsananin kan

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a ci gaba da maida martani kan HKI a yau Asabar ma ta kai hare hare masu tsananin kan cibiyoyin tsaro na HKI dake arewacin kasar falasdinu da aka mamaye.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanan da kungiyar ta fitar a safiyar yau Asabar na cewa dakarun kungiyar sun kai hare hare kan kayakin tsaro na HKI a garin Meron, sannan sun tarwatsa taron sojojin yahudawan a wani wuri tare da amfani da makaman da suka dace.

A jiya ma dakarun kungiyar sun cilla makamai masu linzami kimani 150 kan arewacin HKI inda suka lalata cibiyoyin tsaron HK da dama. Suka kuma halaka sojojin su.

Bayanan sun kara da cewa dakarun hizbullah sun kai hare hare kan HKI ne don maida martani kan kissan Abutalin wanda ya kasance kwamandan dakarun kungiyar a garin Juwayya na kudancin kasar.

Sannan da maida martani kan kissan kiyashin da sojojin HKI suke aikatawa a kan al-ummar Falasdinu a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments