Kungiyar Hizbullah Ta Godewa Kasar Iran Saboda Tallafawa Kasashen Yankin Asiya Ta Kudu Da Kungiyoyin ‘Mukawama’

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya godewa JMI musamman Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyulkhaminaee saboda tallafin da

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya godewa JMI musamman Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyulkhaminaee saboda tallafin da take bawa kasashen yankin da kuma kungiyoyin da suke gwagwarmaya da HKI.

Tashar talabijin ta Presstva ta nakalto Nasarallah yana fadar haka a lokacin ganawarsa da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani wanda ya ziyarce shi a masaukinsa a birnin Beirut.

Ya kuma kara da cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da kasar takem fama das u daga kasashen yamma amma ta dage kan tallafawa wadannan kungiyoyi masu gwagwarmaya da HKI da mafim yawan abubuwan da suke bukata don ci gaba da gwagwarmaya da HKI.

Nasarallah ya fadawa ministan irin ci gaban da ake samu a yakin da ke faruwa tsakanin wadannan kungiyoyui da kuma HKI tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata, musamman fagen dagan da ke kudancin kasar Lebanon.

Har’ila yau ya sake mika ta’aziyyarsa ga mutanen kasar saboda rashin shugaban Ra’isi da kuma ministansa na harkokin waje Dr Hussain Amir ABdullahiyan a hatsarin jirgin sama na ranar Lahadi 19 ga watan mayun day a gabata.

Bangarorin biyu sun tattauna kan sabbin al-amuran siyasa tsaro da batun yaki a Gaza. Kuma kafin haka Kani ya gana da firai ministan kasar Lebanon Najib Mikati, ministan harkokin wajen kasar Abdullahi Bou Habib da Nabi Berri kakakin majalisar dokokin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments