Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta tura jirgin leken asiri kan gidan fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila
Jaridar Hayom ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi zargin kutsawan wani jirgin saman yaki maras matuki ciki na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon cikin sararin samaniyar haramtacciyar kasar Isra’ilan da nufin daukar hoton gidan Fira Minista Benjamin Netanyahu da ke kudancin birnin Haifa.
Jaridar ta ruwaito cewa: Wani jirgin ruwan sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya hango jirgin sama maras matuki ciki a tsibirin Caesarea kuma yana Shirin daukan hoton gidan fira minista Netanyahu, wanda ke kusa da gabar tekun Caesarea a kudancin Haifa.
Jaridar ta ci gaba da cewa: An hango jirgin ne maras matuki ciki mai yiwuwa na kungiyar Hizbullah a kusa da gidan Fira Minista da ke gabar teku, kuma jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya sun gudanar da shawagi a yankin lamarin da ya Sanya jirgin leken asirin ya gudu.