Kungiyar Hamas ta bukaci a takawa yahudawan sahyoniyya birki a lokacinda suke kutsawa cikin masallacin Al-aksa da sunan gudanar da bukuwan su mai suna ‘ Hanukkah” ko bukukuwan Haske, daga jiya Laraba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Harun Nasirudeen wani Jami’an kungiyar ta Hamas ya na fadar haka, ya kuma kara da cewa, banda yakin da Falasdinawa suke fafatawa da sojojin HKI a Gaza da kuma Yammacin Kogin Jordan, kare masallacin alaksa a matsayin masallaci mai tsarki na 3 ga musulmi wani wajibi ne a kan dukkan musulmi su kare shi.
Nasiruddeen ya kara da cewa yakamata Falasdinawa sun rika taruwa a cikin masallacin don hana yahudawan keta hurumin masallacin, na uku a daraja a cikin addinin musulunci.
A jiya Laraba 25 ga watan Decemba ce, Yahudawan Sahyoniyya suka fara bukukuwansu na ‘Hake’, a cikin masallacin Al-aksa tare da samun tsaro na dubban jami’an tsaron su. Bukin dai zai kai ranar 2 ga watan Jeneru na shekara mai zuwa suna yinsa.