Kungiyar gwagwarmaya ta hamas ta yi tir da matakin da HKI ta dauka na bai wa mastugunan yahudawa yan share wuri zauna na Giv’at Ze’ev dake gabar yammacin kogin jodan a arewa masu yammanci birnin Qudus da ta mamaye matsayin birnin.
A cikin wani bayani da ta fitar a jiya litinin kungiyar hamas tace wannan mataki ne mai wahala matuka ga gwamnatin isra’ila ta dauka na tabbatar da mulkin mallaka na dindindin ba bisa ka’ida ba a yankunan falasdinawa da aka mamaye don ci gaba da fadada mamaya da kuma korar falasdinawa
Kungiyoyin falasdinawa sun kira wannan mataki a matsayin mai hatsarin gaske kuma wani nau’I ne na zalunci a fili , hamas ta jaddada cewa duk wani mataki da isra’ila ta dauka na doka game da fadada matsugunnan yahudawa a gabar yammacin kogin jodan batacce ne kuma keta dokoin kasa da kasa ne da kuma hakin falasdinawa mai cike da tarihi
Daga karshe kungiyar ta falasdinu ta yi kira ga mdd da kasashen duniya da masu rajin kare hakki na duniya da su bibiyi wadannan bayanai da kuma yin Allah wadai, da kuma daukar mataki na tunkarar tsarin isra’ila a matsugunnai da kuma hukumtata kan wananan taka doka da take yi