Kungiyar Hamas Ta Lissafi Sunayen Yahudawa 34 Da Zata Saka A Karon Farko Idan An Cimma Yarjeniya Ta Sulhu A Doha Da HKI

Wani babban Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa kungiyarsa a shirye take ta saki yahudawan Sahyoniyya 34 a mataki na farko na musayar fursinoni da

Wani babban Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa kungiyarsa a shirye take ta saki yahudawan Sahyoniyya 34 a mataki na farko na musayar fursinoni da HKI, idan har an cimma yarjeniyar sulhu da ake tattaunawa a kanta a halin yanzu a birnin Doha na kasar Qatar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto wani babban Jami’in kungiyar na fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma kara da cewa kungiyar zata yi haka ne kawai idan har HKI ta janye sojojinta daga zirin gaza, sannan aka kulla yarjeniyar zaman lafiya ta din din din da ita.  Kungiyar ta bayyana cewa HKI tana ganin hakan ba wani ci gaba ne a wajenta ba, ya zuwa yanzu.

Kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin masu gwagwarmaya da HKI a Gaza sun kama yahudawan Sahyoniyya 250 a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, a lokacinda aka fara yakin Tufanul Aksa. Sannan ta saki 105 daga cikinsu a dakatar da budewa juna wuta na mako guda da kuma musayar fursinonin da aka yi a cikin watan Nuwamban shekarar ta 2023 da ta gabata.

Daga karshen kungiyar ta bayyana cewa Hamas zata sake sauran yahudawan da suke hannunta ne kawai idan HKI ta dakatar da yaki kwata-kwata.

Iyalan wadanda Hamas take tsare dasu a HKi dai suna takurawa Benyamin Natanyaho Firay ministan kasar don ganin an sake sauran yahudawan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments