Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da jaddada cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ba ta da halaccin kula da Masallacin Al-Aqsa
A cikin wata sanarwa da ta fitar ta cikan shekaru 56 da kona masallacin Al-Aqsa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa; Gwamnatin mamayar Isra’ila ba ta da wani hakki ko hurumin iko a kan masallacin Al-Aqsa, tana mai jaddada cewa yunkurin da take yi na shafe Masallacin, ba zai yi nasara ba.
Hamas ta yi kira da a dauki tsauraran matakai na kasashen Larabawa da na Musulunci don kare birnin Qudus da Masallacin Al-Aqsa da kuma tunkarar shirin gwamnatin mamayar ‘yan ta’addan yahudawa. Rahotonni suna nuni da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta na ci gaba da tsananta laifukan yaki da take yi kan al’ummar Falasdinu, musamman a yankin zirin Gaza, inda mazauna yankin ke fama da ci gaba da killacewa da yunwa.
Wannan bikin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da zafafa kai hare-hare, tun bayan kona Masallacin Al-Aqsa a ranar 21 ga watan Agustan shekara ta 1969. Kungiyar Hamas ta tabbatar da cewa laifukan ‘yan mamayar ba za su yi nasarar kafa wata sabuwar hujja da za ta ba ta damar kwace wani bangare na masallacin Al-Aqsa ba.