Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ki amincewa da batun ficewa daga Gaza
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa; “Tana fatan samun sakamako mai kyau daga gwamnatin Amurka dangane da batun tsagaita bude wuta a Zirin Gaza.”
Babban jami’in kungiyar Hamas, Osama Hamdan ya sanar da cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ki amincewa da batun ficewa gaba daya daga Zirin Gaza da kuma dakatar da ayyukan soji a zaman tattaunawan da ake yi tsakanin bangarorin da ke shiga Tsakani.
Hamdan ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas ta dauki matakin yin sassauci game da batun musayar fursunoni, muddin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da batun tsagaita bude wuta, janyewa gaba ɗaya daga Zirin Gaza, shigar da agaji cikin Gaza da kuma tsara sake gina yankin na Gaza ba tare da gindaya sharadi ba.