Kungiyar Hamas Ta Ce Mai Yuwa Tsagaita Wuta A Lebanon  Ya Zama Sharar Fage Na Tsagaitata A Gaza

Wani babban jami’i na kungiyar Hamas ya bayyana cewa kungiyar tana aiki kud da kud da yar uwanta na kungiyar Hizbullah a Lebanon a yakin

Wani babban jami’i na kungiyar Hamas ya bayyana cewa kungiyar tana aiki kud da kud da yar uwanta na kungiyar Hizbullah a Lebanon a yakin da suke fafatawa da HKI sannan mai yuwa tsagaita wuta da aka samu a Lebanon ya zama sanadiyyar tsagaita ta a Gaza nan ba da dadewa ba.

Tashar Talabijanta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sami Abu-Zuhra na kungiyar Hamas yana fadawa tashar talabijan ta AL-Alam da ke watsa shirye-shiryensa da harshen larabci a nan Teran haka a jiya Alamis.

Abu-Zuhr ya kuma taya kungiyar hizbullah murnar tsagaita wuta a Lebanon ya kuma kara da cewa hakkin mutanen Lebanon ne a dakatar da ruwan boma-bomai a kansu.

Ya ce kungiyar Hamas tana jinjinawa kungiyar Hizbullah saboda tallafawa mutanen Gaza na kimani watanni  14 a fafatawan da su ke yi da sojojin HKI. Abu Zuhri ya kara da cewa: gwamnatin HKI ta kasa cimma manufofinta ta yakar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon. Don haka wannan nasara ce a fili ga kungiyar Hizbullah da kuma mutanen kasar Lebanon. Gwamnatin HKI ta farwa Hizbulla da yaki ne saboda samar da zaman lafiya mai dorewa a kudancin kasar Lebanon sannan ta maida yahudawa mazauna arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa matsugunansu, amma ta kasa yin haka har aka tsagaita wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments