Search
Close this search box.

Hamas: Kisan Haniyah Ya Kara Mana Karfi Da Himma

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: Kisan gillar da aka yi wa shahidi Isma’il Haniyah ya kara karfi da himman ‘yan gwagwarmaya Kungiyar

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: Kisan gillar da aka yi wa shahidi Isma’il Haniyah ya kara karfi da himman ‘yan gwagwarmaya

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fitar da sanarwar cewa: Kisan gillar da aka yi wa mujahidi Isma’il Haniyah, babu abin da zai karawa kungiyar Hamas, sai karfi da azama da kuma tsayin dakan Falastinawa na ci gaba da tafarkinta, sannan kuma jinin shahidi Haniyah mai tsarki zai ci gaba da kara kaimi da jajurcewar ‘yan gwagwarmaya.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Tun a farkon sa’o’in kai harin kisan gilla kan Isma’il Haniyah da yahudawan sahayoniyya suka yi, ofishin siyasar kungiyar Hamas da kwamitin shurar kungiyar sun yi kira da a gudanar da taron gaggawa, inda suka tattauna batutuwa masu muhimmanci da hakkin da ya rataya kan kasashen duniya. Kuma bayanin ya ci gaba da cewa kisan gillar da aka yi wa mujahidi Isma’il Haniyah babu abin da kara wa kungiyar Hamas, sai karfi da azama da kuma tsayin daka wajen ci gaba da tafarkinsa, kuma jininsa tsarkakakke zai kara ruruta wutar juriya da kara kaimi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments