Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta jaddada cewa: Bayyanar yunwa a Gaza laifi ne na yaki da ke bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta bayyana damuwarta kan rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar dangane da yaduwar yunwa a zirin Gaza.
Kungiyar ta dora wa hukumar ‘yan sahayoniyya ‘yan mamaya, cikakken alhakin wannan laifi da kuma sakamakonsa, tare da la’akari da shi a matsayin wani sakamako kai tsaye na laifukan yunwa, killace al’umma ba bisa ka’ida ba, barna da ruguza tsari da hana kai agaji, wadanda dukkaninsu suke cikin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Asabar, kungiyar ta jaddada cewa, ayyana yunwar, wani gargadi ne ga duniya kan wanzuwar laifukan jin kai, da siyasa, da na shari’a da ke bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa da ba a taba gani ba. Ta yi kira da a dauki dukkan hanyoyin gaggawa na kasa da kasa don tabbatar da isar da kayan agaji da abinci cikin gaggawa, cikin aminci, ba tare da hana ruwa gudu ba, don ceto rayukan fararen hula da suka makale a zirin Gaza.
Kungiyar ta jaddada wajibcin mika fayil din laifuffukan killace Gaza da kakaba yunwa da yahudawan sahayoniya suka aikata da kuma yunwar da suka haddasa a Gaza zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.